Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a wani yunƙuri na yin garambawul ga muƙamen gwamnatin jihar ya tsige sakataren gwamnatinsa Dakta Baffa Bichi da shugaban ma’aikatan gwamnati da ƙarin kwamishinoninsa guda biyar a jihar.
Kwamishinonin da gwamnan ya sauke sun haɗar da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Baba Halilu Dantiye, da Kwamishinam Kuɗi, Ibrahim Jibril Fagge da Kwamishiniyar Al’adu da yawon bude ido, Ladidi Ibrahim Garko.
Sai kuma Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Shehu Aliyu ‘Yammedi, da Kwamishinan Raya Karkara, Abbas Sani Abbas.