Gwamnan Kano ya bukaci kwamishinonin da aka yiwa sauyin wuraren aiki da su fara aiki ranar Talata

Abba Kabir Yusuf sabo 1

 

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci dukkan kwamishinonin da aka yi wa sauyin wuraren aiki da su kammala mika mulki da kama sabbin ayyukansu zuwa ranar Talata, 17 ga Disamba, 2024.

Da yake magana ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa, Gwamnan ya jaddada cewa sauye-sauyen da aka yi a majalisar zasu fara aiki ne gaba ɗaya a taron majalisar zartarwa na jiha da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba, 18 ga Disamba, 2024.

Ya kuma ja hankalin kwamishinonin kan mahimmancin kammala dukkanin matakan sauya wurin aiki kafin wannan lokaci.

“Dukkan kwamishinonin da sauyin ya shafa an umarce su da su mika ragamar ayyukansu tsakanin Litinin, 16 ga Disamba da Talata, 17 ga Disamba, 2024,” in ji sanarwar.

Haka zalika, Gwamnan ya bukaci mambobin majalisar zartarwa ta jiha da su kara kaimi wajen aiki tare da nuna kishin aiki domin ci gaban al’ummar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here