Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta cimma yarjejeniya da ƙasar Saudiyya don ganin an kara samun nasarar kwato kadarorin gwamnati da aka sace.
Shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa, yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Jeddah da hukumar yaki da rashawa ta Saudiyya NAZAHA, ya ce hakan zai taimaka wajen dakile masu aikata rashawa.
Abubuwa da shugaban na EFCC da tawagarsa suka tattauna a takwarorinsu na Saudiyya a ziyara da suka kai, ya hada da yadda za a kara kaimi wajen kwato kadarori da wasu ke sacewa su kai kasar.
Bawa ya ce za a samu nasara ne kadai ta hanyar tattara bayanan sirri da samun bayanai a kan lokaci daga wajen hukumomi masu yaki da rashawa da kuma takwarori na kasashen waje.












































