Uwar Jam’iyyar APC ta jingine korar da reshenta na Jihar Gombe ya yi wa tsohon gwamnan jihar, Sanata Danjuma Goje, kan zargin zagon kasa a zaben da ya gabata.
Sakataren Yada Labaran uwar jam’iyyar APC, Felix Morka, ya shaida wa ‘yan jarida a Abuja cewa, jami’iyyar ta jingine hukuncin da reshenta na jihar ya dauka a kan Sanata Goje, da nufin sake nazarin batun.
Felix Morka ya ce, Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar (NWC) ne zai sake nazari kan abubuwan da suka kai ga daukar matakin korar Goje a Gombe, amma har yanzu shi halastaccen dan jam’iyyar ne.
Ya ce uwar jam’iyyar ta damu saboda yawaitar matakin ladabtarwa da rassan jam’iyyar na jihohi ke dauka kan zargin mambobi da laifuka, ciki har da a lokacin zabukkan da aka kammala.













































