Buhari zai ziyarci jihar Zamfara ranar Alhamis

President Buhari 2 1062x598 1
President Buhari 2 1062x598 1

A gobe Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki ta yini daya a jihar Zamfara.

Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar kuma shugaban kwamitin yada labarai na ziyarar ta shugaban kasa, Alhaji Ibrahim Dosara ya rabawa manema labarai a Gusau ta tabbatar da hakan.

Sanarwar ta ce, gwamnatin jihar ta yi isassun tsare-tsare don karbar bakuncin shugaban kasa, inda ta kara da cewa, hukumomin sun tsara matakan tsaro da suka dace don ganin ba’a samu cikas a yayin ziyarar ba.

Ta kuma gargadi mutane game da daukar duk wani makami da suka hada da ashana, wuka da sanduna ko duk wani tutoci wanda zai iya janyowa jihar abun kunya.

A cewar sanarwar, an kuma gargadi mutane kan ajiye motoci ba bisa ka’ida ba, saboda an umurci jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC da su kwashe duk motocin da suka karya doka tare da bayyana su domin gurfanar da su gaban kuliya.

Ya kara da cewa Gusau kasancewar babban birnin jihar zai kasance a rufe ga masu ababen hawa na tsawon sa’o’i uku da ziyarar za ta dauka, inda ta kara da cewa za a rufe dukkan wuraren ajiye motoci a Gusau har sai bayan tafiyar shugaban kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here