Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja a ranar Larabar ta umurci gwamnatin tarayya da ta mayar wa jihar Rivers kason kudaden da aka zaftare daga asusun tarayya domin tallafawa asusun ‘yan sandan Najeriya.
Alkalin kotun, Mai shari’a Ahmed Mohammed ya yanke hukuncin ne a wata kara da babban mai shari’a na jihar Ribas ya shigar a shekarar 2020, kan babban lauyan gwamnatin tarayya, Akanta Janar na Tarayya, Ministan Kudi da sauran su.
Idan dai za a iya tunawa, a shekarar 2020 gwamnatin jihar Ribas ta bukaci kotu da ta bayyana cewa kudaden da ke cikin asusun tarayya “ana iya raba su ne a tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi a kowace jiha ta Najeriya ba kai tsaye ga kowace hukuma ta gwamnatin tarayya ba. ciki har da rundunar ‘yan sandan Najeriya.”










































