Tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Sanarwar nasa na zuwa ne bayan tsohon jagoran jam’iyyar All Progressives Congress APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, Dan Majalisar Dattawa, Orji Kalu, da tsohon Gwamnan Imo, Rochas Okorocha, sun bayyana irin wannan bukata.
Tsohon Gwamnan na Kwara ya ce yana da kwakkwaran tarihi na bayarwa da gogewa wajen yanke hukunci mai tsauri.
An haifi Saraki a ranar 19 ga Disamba, 1962, dan Sanata ne a jamhuriya ta biyu, marigayi Olusola Saraki.
An fara zabar shi a Majalisar Dattawa a 2011 kuma ya zama Shugaban Majalisar Dattawa a 2015.
A shafin sa na Facebook, Saraki ya ce: “Tun da farko na amsa ma wani mabiyi na a shafin Twitter wanda kamar dubunnan ku ke ta fafutukar ganin an hada kan #RescueNigeria.
“Yayin da muke shirin fara sabuwar tafiya nan gaba, ina fatan za mu hada karfi da karfe domin samun tikitin babbar jam’iyyar mu ta PDP, da kuma gina kasa mai aiki da mu baki daya.












































