Kundin tsarin mulkin Najeriya ya amince da sanya hijabi ga mata musulmi – Minista

IMG 20220207 WA0000
IMG 20220207 WA0000

 

Gwamnatin tarayya ta ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa mata musulmi damar sanya hijabi daidai da koyarwar addininsu.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana haka a wajen taron tattaunawa da kungiyar hadin kan mata musulmi ta Najeriya ta shirya a wani bangare na bikin ranar Hijabi ta Duniya na bana, wanda aka gudanar a Abuja.

Adamu ya ce an kyale duk ‘yan kasa su rika gudanar da addininsu matukar hakan ba zai kawo wata matsala ba.

Ministan wanda ya samu wakilcin Hajiya Sidikat Shomope ta sashin wayar da kan jama’a a hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa (UBEC), ta ce abin takaici ne yadda ake cece-kuce kan saka hijabi a kasar nan har matakin ke haifar da fadace-fadace.

Idan dai za a iya tunawa, an samu tashin hankali a ranar Alhamis a makarantar sakandaren Baptist dake Ijagbo a karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara, wanda ya kai ga kashe Habeeb Idris, dalibin makarantar, yayin da wasu ‘yan daba suka tarwatsa taron da daliban makarantar suka yi.

Adamu ya ce: “Sanya hijabi da mata musulmi ke yi sunna ne kamar yadda Alqur’ani ya tabbatar .” (Sura ta 33, aya ta 59).

Ministan ya ce akwai abubuwa da yawa da kasar za ta iya samu ta hanyar tattaunawa kan batutuwan da suka shafi addini maimakon tayar da hankali.

“’Ya’yanmu za su kasance ’yan Najeriya ba tare da la’akari da imaninsu ba. Za su rayu da mu’amala a duniya a wajen makaranta inda babu iyaka tsakanin addinai.

“Ya kamata mu fahimci cewa kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ya ba wa ‘yan kasa yancin yin addini. Wannan, a ma’ana, yana nufin cewa an ƙyale duk ’yan ƙasa su yi addininsu bisa koyarwar imaninsu matuƙar ba a samu wata cuta ko damuwa ga wasu mutane ba.”

Adamu Adamu ya yi kira ga daukacin shugabannin gargajiya, addinai da kuma shugabannin al’umma da su yi amfani da ofisoshinsu wajen dakile tashe-tashen hankula domin ‘yan Nijeriya su zauna lafiya da juna da kuma zaman lafiya.

Ministan ya kuma yi kira ga iyaye da malaman makaranta “da su tabbatar da cewa a cikin kalmomi da ayyuka, sun gabatar da mafi kyawun abin koyi ga yaranmu da za su yi koyi da su.”

Daraktan kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC), Farfesa Ishaq Akintola, wanda ya yi magana kan ‘matsayin Hijabi’, ya yi nuni da cewa hakki ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa, musamman gwamnati a kowane mataki, ta tabbatar da ganin an samu ‘yancin walwala, dukkan mata musulmi suna da kariya don yin ado da hijabi a cikin jama’a.

Shugabar kwamitin majalisar wakilai kan harkokin zabe, Aisha Duku; Hajiya Maryam Bukar Abba; Mataimakiyar shugabar gwamnati a jami’ar jihar Nasarawa dake Keffi, Farfesa Saadatu Hassan Liman; Farfesa Rafatu Abdulhamid na Jami’ar Abuja da kuma FOMWAN Ameerah ta kasa Hajiya Rafat Sanni sun bukaci mata musulmi masu sanye da hijabi da su tabbatar da cewa yayin da hijabin ya rufe kamannin jikinsu, an kuma ba da fifiko kan rayuwarsu da dabi’unsu.

Uwargidan tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, Hajiya Amina ta ce: “Zamu kara azama wajen wayar da kan mu da inganta wannan dabi’a ta Musulunci ba tare da tsoratarwa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here