Jami’ar Jihar Chicago ta ce jagoran jam’iyyar APC kuma dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, ya halarci jami’ar.
Beverly Poindexter, wanda ke kula da takardun shaidar kammala karatun digiri a ofishin magatakarda, ya bayyana hakan a cikin martanin sakon Email ga Jaridar PUNCH ranar Talata.
“Tinubu ya halarci jami’ar mu, duk da haka, idan ana buƙatar ƙarin bayani, je zuwa shafin yanar gizon studentclearinghouse.org don yin bincike,” in ji Poindexter.
A wata wasika da ta rubuta a ranar 20 ga watan Agusta, 1999 mai dauke da sa hannun magatakarda na lokacin, Lois Davis, jami’ar ta bayyana cewa Tinubu dalibinta ne tsakanin 1977 zuwa 1979.
Ya rubuta cewa, “Yana da kyau ku sani cewa Bola A. Tinubu ya halarci Jami’ar Jihar Chicago daga watan Agusta 1977 zuwa Yuni 1979. Ya samu lambar yabo a ranar 22 ga Yuni, 1979. Ya karanci ilimin hada-hada da sarrafa kudade wato Accounting.
Solacebase ta ba da rahoton cewa sama da shekaru goma ana ta samun cece-kuce dangane da makarantar da Tinubu ya halarta.
Lauyan kare hakkin bil’adama, Cif Gani Fawehinmi (SAN), shi ma ya tuhumi Tinubu a kan sahihancin sa, ya kuma kai karar rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa rashin bincikensa.
Kotun koli a hukuncin da ta yanke a ranar 10 ga Mayu, 2002 ta yanke hukuncin cewa ‘yan sanda ba za su iya gurfanar da Tinubu a gaban kuliya ba kan zargin gabatar da takardar kammala karatu ta bogi.













































