Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 100 don tallafa wa sojoji da suka jikkata da kuma iyalan sojojin da aka kashe a hare-haren da ake kai wa a jihar.
Gwamnan ya bayar da tallafin ne a ranar Asabar yayin wata liyafar cin abinci ta bikin babbar Sallah da ya shirya tare da hadin gwiwar babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede da babban hafsan sojin sama Air Marshal Hassan Abubakar, a Maimalari Cantonment da ke birnin Maiduguri.
Zulum ya mika cakin Naira miliyan 100 ga kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, domin bayar da Naira 500,000 ga kowane sojan da ya samu rauni, da kuma raba sauran kuɗin ga iyalan sojojin da suka mutu a bakin aikin.
An gabatar da jawabin ne a gaban Oluyede, Abubakar da kwamandan rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa MNJTF Manjo Janar Godwin Mutkut.












































