Na yi dacen zabar ka a matsayin mataimakin shugaban kasa – Tinubu ya shaida wa Shettima @59

President Bola Tinubu and Vice President Kashim Shettima 750x430 (1)

Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima murnar cika shekaru 59 a duniya, inda ya bayyana shi a matsayin abokin tarayya mai aminci kuma amintaccen abokin hadin kai a kokarin da ake na gina Najeriya mai ci gaba.

Ya ce bai yi kuskure ba wajen zaben sa a matsayin mataimakinsa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ya fitar kuma mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya raba.

“Yau, Satumba 2, 2025, ta sake ba ni wata dama ta musamman don taya ka murnar ɗan’uwana, abokin tarayya, mataimakin shugaban ƙasa, yayin da kake bikin tunawa da ranar haihuwa,” in ji Tinubu.

Ya yabawa Shettima bisa sadaukarwa da jajircewarsa tun lokacin da ya shigo da shi kan wannan tafiya ta maido da kasar nan bisa turba.

“Ka yi wa al’ummar Borno hidima, jiharka ta haihuwa, da kyau a matsayin gwamna na tsawon shekaru takwas sannan daga baya a matsayin Sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya a Majalisar Dokoki ta kasa.

Karin labari: Kofa ya shirya addu’o’i na musamman ga Tunubu, tare da tallafawa matasa 3,000

Duk da haka, hidimar da kake yi wa Najeriya, sakamakon kishin ka na dimokuradiyya, da shugabanci na gari, da bunkasar tattalin arziki, ya fi daukar hankali,” inji shi.

Shugaban ya kuma nuna jin dadinsa ga goyon bayan Shettima da hadin gwiwar gudanar da mulki.

Ina matukar godiya da hazakar ka, amincinka, hadin gwiwa, da goyon bayanka a matsayin mataimakina. A lokacin da na zaɓe ka a matsayin abokin tarayya, na zaɓi ƙwarewa da sauran halaye waɗanda Najeriya za ta dogara da su.

Shugaban ya kara da cewa, “Dole ne mu ci gaba da yin aiki don ganin an tabbatar da shirin sabunta bege, wanda zai samar da ci gaba a kasar da kuma inganta rayuwar jama’armu.”

Tinubu ya kuma bayyana dangantakarsa da Shettima a matsayin wacce ta wuce bukatun ofis, domin ya yi masa fatan alheri da cika shekaru 59 a duniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here