Khalid Al-Barnawi wanda yasa bom a shalkwatar UN, na daya daga cikin wadan da suka gudu daga gidan yarin Kuje

Khalid al Barnawi 750x430 1
Khalid al Barnawi 750x430 1

Muhammad Usman wanda aka fi sani da Khalid al-Barnawi, shugaban kungiyar Ansaru, wanda suka sa bom a shelkwatar UN 2011 a Abuja, inda da suka kashe mutum 18 yayin da mutum 100 suka raunata, na daya daga ciki wadan da ‘yan Boko Haram suka kubutar daga gidan yari Kuje.

Wani jami’i wanda baya so a bayyana sunan sa ya ce, Al-Barnawi na iya kasan cewa wanda ya shirya fashin magarkamar ta Kuje, saboda kasan cewar sa kwararre wajin ta’addanci.

Guduwar Al-Barnawi na nuni da alama cewa harkokin ‘yan boko haram na iya cigaba a Najeriya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here