Labari da dumi dumi: Peter Obi ya zabe wanda zai masa mataimaki

Datti Baba Ahmed unveiling as LP Vice Presidential Candidate 750x430 1
Datti Baba Ahmed unveiling as LP Vice Presidential Candidate 750x430 1

 Tsohon dan takarar shugabacin kasa a jam’iyar PDP, Datti Baba-Ahmed ya zama wanda zai yiwa Peter Obi mataimaki a jam’iyar LP.

Peter Obi ya sanar da zabar Baba-Ahmed a matsayin mataimakin sa yau Juma’a a Abuja.

Jaridar solacebase ta rawaitu cewa Datti Babba-Ahmad dan shekara 46, wanda shine ya kafa jami’ar Baze dake Abuja, tsohon dan majalisar waikilai ne wanda ya wakilci karamar hukumar Zaria daga 2003 zuwa 2007.

An kuma zabe shi a matsayin sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa, ya sami digirin sa a jami’ar Maiduguri akan tsimi da tanadi (Economics).

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here