Ina farin cikin ganin ’yan adawa a cikin rudani- Tinubu

Bola Tinubu budget

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya caccaki jam’iyyun adawa inda ya bayyana cewa abun farin ciki ne ganin yadda jam’iyyun PDP da Labour ke cikin rudani.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yau Alhamis yayin wani zama na hadin gwiwa da majalisar dokoki ta yi domin bikin ranar dimokuradiyya na bana, inda ya kuma yi maraba da wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar adawa zuwa jam’iyyar APC.

“Dukkanku muna maraba da ku zuwa ga ci gaba, Babu wanda ya isa ya rufe kofa,” in ji Tinubu a kaf a cikin rarrabuwar kawuna da ke addabar jam’iyyun adawa.

Shugaban ya yi tsokani jam’iyyun da ga dukkan alamu sun girgiza da sauya sheka da kuma sa-in-sa a siyasance, inda ya ce maimakon firgita, kamata ya yi su shigo cikin tafiyarsa.

“Jam’iyyun siyasar da ke tsoron barin mambobin su na iya zama mafi kyau a yi amfani da su ta hanyar nazarin ayyukansu da al’amuransu, maimakon tsoratar da su in ji shi.

A cikin wani karin magana mai tsokaci, Tinubu ya kara da cewa, “A gare ni, ba zan ce, ku yi kokarin gyara gidanku ba, Ni ma ba zan taimake ku ba.
Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke nuni da cewa al’amuran na kara tabarbarewa a tsakanin jam’iyyun PDP da LP, inda wasu jiga-jigan ‘yan jam’iyyar suka nuna rashin gamsuwa tare da neman zabin jam’iyyar APC mai mulki.
Kalaman na Tinubu dai sun janyo cece-ku-ce daga ‘yan majalisar da suka halarci zaman, inda ‘yan jam’iyyar APC suka yaba da yadda ‘yan adawa suka nuna rashin jin dadinsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here