Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fasan Yamma, sun ce sun kashe ‘yan ta’adda da dama a wani gagarumin farmaki da suka kai a yankin Kalgo da kewayensa a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Daraktan yaɗa labarai na rundunar Manjo Janar Markus Kanye, ne ya bayyana hakan yau Alhamis a Abuja.
Kangye ya ce, wani ɗan ta’adda da aka fi sani da Auta tare da abokansa Abdul Jamilu da Salisu daya, su na daga cikin wadanda aka kashe a arangamar.
A cewarsa, wadannan ‘yan ta’adda na da alaka da ta’addanci da dama a yankin baki daya.
Kangye ya ce, a wata arangama da sojojin suka yi sun kashe karin ‘yan ta’adda 10 da suka taru a kusa da wani gidan mai a Danjibga.
Ya kuma ce, ana kyautata zaton ‘yan ta’addan na cikin kungiyar da Dogo Sule ya hada kai domin kai hari.
“Rundunar Sojin Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da kuma dawo da zaman lafiya a fadin Zamfara da yankin Arewa maso Yamma.
“Wannan farmakin ya na jaddada kudurinmu na wargaza hanyoyin sadarwar ‘yan ta’adda da kuma gurfanar da masu aikata laifuka a gaban kuliya,” in ji shi.













































