Ministan harkokin cikin gida Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya sha alwashin kawar da cin hanci da rashawa a gidajen gyaran hali tare da tabbatar da cewa cibiyoyin da ke fadin kasar nan sun mayar da hankali wajen gyarawa maimakon hukunta su.
Tunji-Ojo ya yi wannan alkawarin ne a ranar Larabar a Abuja, yayin taron jin ra’ayin jama’a karo na biyu kan zargin cin hanci da rashawa da wasu laifukan da ake yi wa hukumar gyaran hali ta Najeriya NCoS.
Ministan ya ce matakin wani bangare ne na kokarin da gwamnati ke yi na mayar da aikin gyaran hali a matsayin abin koyi na gyaran hali da tarbiyya.
Ya kuma jaddada cewa gwamnati ta dukufa wajen canza sheka na hukumar gyaran hali wanda a baya ya yi fama da zarge-zargen cin hanci da rashawa da rashin kulawa.
Karin karatu: Zargin badaƙala: Kotu ta tsare tsohon shugaban NHIS a gidan gyaran hali na Kuje
A cewarsa, babban nauyin da ke kan jami’an gidajen gyaran hali shi ne ya zama wakili na gyara tarbiyya.
Ministan cikin gida ya jaddada cewa gwamnati mai ci a karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ta himmatu wajen samar da isassun kayan aiki da kudade domin aikin gyaran.
Ya ce gwamnatin tarayya ta kuma ba da tabbacin cewa za a horar da jami’an gyaran halimi da kuma samar da kayan aiki don kulawa ga bukatun fursunonin.
Don haka Tunji-Ojo ya bukaci kwamitin binciken da ya binciki al’amuran da suka shafi cin hanci da rashawa, cin zarafi da rashin kula da aiki a gidajen gyaran hali tare da bayar da shawarwarin kawo gyara.(NAN)