Yanzu-Yanzu: An yi garkuwa da dattawan 50 da suka je sulhu da Jagoran ‘Yan Fashin Daji a Zamfara

bandits 1 750x430 (1)

An yi garkuwa da kusan dattawa 50 daga kauyen Magamin Diddi a Mazabar Magami/Faru ta Karamar Hukumar Maradun yayin da suke kan aikin sulhu.

An ce jagoran ‘yan fashin daji mai suna Jammo, wanda ke kula da dazukan Muntsira a Maradun ta Jihar Zamfara ne ya yi garkuwa da su.

Shugaban Karamar Hukumar Maradun, Hon. Bello Dosara, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust, amma ya ce mutanen da kansu suka yanke shawarar ganawa da jagoran ‘yan fashin ba tare da izinin gwamnati ba.

“Mun ki sulhu da ‘yan fashin daji, kuma Gwamna Dauda Lawal bai taba goyon bayan hakan ba, amma ba tare da sanin mu ba mutanen sun zabi su yi hakan.” In ji Dosara.

Dosara ya kara da cewa jagoran ‘yan fashin ya rufe hanyar shiga kasuwa ga kauyen, amma shi ya rika ba su tsaro kowane mako don su je kasuwa su dawo gida lafiya.

“Na yi mamaki yadda suke zuwa su hadu da makiyansu, sun rufe musu hanyar kasuwa, ni kuma ina ba su tsaro kowane mako,” in ji Dosara cikin damuwa.

Shugaban karamar hukumar ya kuma tabbatar da sakin mutane 11, yayin da sauran 39 har yanzu suna hannun ‘yan fashin dajin.
“Ya saki wasu ne kawai domin su sanar da mutane lamarin da ya faru,” in ji shi.

A nasa bangaren, Kansilan Mazabar Magami/Faru, Bello Husseini, ya bayyana cewa da farko jagoran ‘yan fashin daji Jammo, wanda ke tayar da hankali a yankin, ya fafata da jami’an tsaron jihar Zamfara ‘Askarawa’ inda suka kashe mataimakansa biyu suka kwaci bindigogi.

Sai dai a lokacin Azumin da ya gabata, ‘yan fashin da suka kai hari na ramuwar gayya ma sun kashe jami’an Askarawa biyu suka kwaci bindigogi suma.

Husseini ya kara da cewa jagoran ‘yan fashin ya nemi sulhu bayan an kashe daya daga cikin mutanensa a wani harin sojoji na baya-bayan nan a kauyen Kandare, abin da mutanen suka amince da shi da kansu sabanin dokar gwamnati.

A cewarsa, al’umma sun tura kwamitin mutane 50, bayan sun isa sai Jammo ya ci amanarsu ya kuma yi garkuwa da su amma daga baya ya saki mutane 11, inda ya neman Naira miliyan 24.

“Mun ki kowace irin sulhu saboda mun san ba abu bane da zai dore, zasu iya fadar magana dari ta karya kafin au fadi daya ta gaskiya.”

“Mutanen da ya tsare tsofaffi ne, babu dalilin da zai sa ya tsare su; ya rike su da cewa ya gaji da fashin daji ya zabi sulhu,” in ji Husseini.

Shugaban karamar hukumar da Kansilan sun roki gwamnati da jami’an tsaro da su kai hari “Dajin Natsira” saboda ‘yan fashin ba su taba fuskantar hare-hare ba a duk tarihin fashin daji a Jihar Zamfara.

Sun kuma roki Gwamna Lawal da Ministan Tsaro na Jihar Bello Matawalle su kawo agajinsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here