Gwamnatin Jihar Kano, a ranar Talata, ta yi taro da mambobin kungiyan ASUU na jami’o’in jiha guda biyu suna neman a dakatar da yajin aiki, kmar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
Rahotanni sun nuna cewa an yi taron ne tsakanin jami’an gwamnati da mambobin ASUU daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha (KUST), Wudil, da Jami’ar Yusuf Maitama Sule (YUMSUK).
Taron, wanda aka yi na awanni an tashi ba tare da cimma matsaya ba amma an yi alkawarin za a sake zama cikin sati daya.
Shugaban ma’aikatan jihar Kano, Usman Bala Muhammad, ya roki kungiyar har ya bukaci mambobin su tambayi shugabanninsu su fita daga ASUU na tsawon wata uku. Amma, ya bawa kungiyar sati daya su tattauna kan hanyoyin da ya dace – domin a cigaba da karatu a makarantar.
Da ya ke magana bayan taron kan ko gwamnatin jihar tana shirin daukan mataki kan lakcarorin da ke yajin aiki, shugaban ma’aikatan ya ce a yanzu babu wani shiri a yanzu amma gwamnatin za ta dauki mataki idan abubuwa suka cigaba a hakan.













































