Gwamnatin jihar Kogi ta rufe dukkan makarantu domin shirye-shiryen zaben gwamnan Jihar

Yahaya Bello students
Yahaya Bello students

Gwamnatin jihar Kogi ta bada umarnin da a rufe dukkan makarantun dake fadin jihar, a wani bangare na shirye-shiryen zaben gwamnan jihar da aka shirya gudanarwa a ranar asabar 11 ga watan Nuwambar, shekarar da muke ciki ta 2023.

Kwamishinan ilimi na jihar Mista Wemi Jones, ne ya bada umarnin ranar Laraba ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Lokoja babban birnin Jihar ta Kogi.

Ta cikin sanarwar ma’aikatar ilimi, kimiyya da fasaha ta jihar ta bada umarnin da a rufe daukacin makarantun Firamare da sakandire da kuma manyan makarantun gaba da sakandire da fadin jihar daga ranar Juma’a 10 ga watan Nuwamba, zuwa ranar Talata 14 ga watan na Nuwamba.

A cewar kwamishinan ana sa ran dukkan makarantun dake fadin jihar da suka hadar da na gwamnati da masu zaman kansu cewa zasu rufe makarantun kamar yadda aka umarta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here