Jami’ar Bayero da ke Kano ta musanta labarin da ake yadawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo da ke bayyana cewa ta yi karin kudin makaranta.
A cikin wata sanarwa da Lamara Garba, mataimakin magatakarda mai kulada hulda da jama’a ya fitar ranar Litinin ta ce wasikar karya ce.
Sanarwar ta ce har yanzu mahukuntan jami’ar ba su yanke hukunci kan duk wani karin kudin makaranta ba sabanin yadda wasu marasa gaskiya ke yayata labaran a shafukan sada zumunta.
“Ya kamata dalibai da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki su lura cewa har yanzu Jami’ar Bayero ba ta yanke shawara kan karin kudin makaranta ba sabanin yadda wasu marasa tunani ke yada labaran a kafafen sada zumunta,” in ji sanarwar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa jami’ar ta bukaci jama’a da su yi watsi da wannan bayanin a matsayin na bogi.













































