Masari ya fidda Naira Milyan 500 domin karban bakuncin Shugaba Buhari.

Governor Masari
Governor Masari

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya amince da cire sama da Milyan 499 daga asusun hadin gwiwa na jihar domin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ayarin taron yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu a jihar.

Wata majiya ta bayyana cewa ana sa ran Buhari zai jagoranci jiga-jigan jam’iyyar APC da magoya bayan jam’iyyar a Katsina tsakanin ranakun Juma’a da Asabar 26 da 27 ga watan Janairun 2023.

Gabanin taron, wata majiya tace anyi zargin aikewa da Kwamishinan Kananan Hukumomin Jihar Katsina da kuma Harkokin masarautu da sakatariyar dindindin domin sanya hannu da tabbatar da cire makudan kudade daga asusun hadin gwiwa na kananan hukumomi.

“An umurce ni da na mika bukatar mai lamba S/MLGCA/GEN/259/C/IV ta 17” Janairu 2023 da kuma isar da amincewar mai girma Gwamna, na a saki Nera Milyan N14,695,588 ga kowane mutum 34.

Kananan Hukumomin sun kai N499,650,000.00 (Miliyan dari hudu da casa’in da tara, Naira dubu dari shida da hamsin kacal) daga cikin ma’auni na kananan hukumomi 34 dake cikin asusun hadin gwiwa na kananan hukumomi domin baiwa kananan hukumomin damar samar da isasshiyar hadakar ‘yan kasa, su karbi bakuncin shugaban kasa a ziyarar aiki jihar Katsina daga ranar 26 zuwa 27 ga watan Janairu, 2023.

Idan za’a tuna a baya kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ta bayyana cewa shugaba Buhari zai jagoranci magoya bayan jam’iyyar a yakin neman zaben Tinubu a fadin jihohi 10 na tarayyar kasar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here