Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da sauran laifuffuka ta kasa, ta gano yadda dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Nassarawa ta jihar Kano, ya mayar da motar da aka saya domin ayyukan mazaba zuwa na amfaninsa na kansa.
Mataimakin sufritandan ofishin hukumar a jihar Kano, Bukar Galadima ne ya bayyana haka ga Solacebase a ranar Talata, bayan jami’an hukumar sun bibiyi motar ta ayyukan mazaba da aka boye a wani wuri a kwaryar birni.
Solacebase ta ruwaito cewa, shugaban tawagar bibiyar ayyukan mazabu na hukumar ICPC, ya yi zargin cewa, motar da dan majalisar ya saya da sunan ayyukan mazaba domin amfanin al’umma, ta koma na amfaninsa na kashin kai.
Ya kara da cewa, hukumar ta kwace motar domin ci gaba da bincike.
Ya ce “mun gano cewa an fitar da kimanin naira miliyan 13 domin sayen motar pickup kirar Ford 2019 daga cikin kasafin kudin ayyukan mazaba”
A cewar Galadima, da zarar an kammala bincike, hukumar za ta gurfanar da dan kwangila tare da dan majalisar saboda karkakatar da akalar motar da suka yi.
Idan za a iya tunawa, a baya-bayan nan ne ICPC ta fara binciken ayyukan mazabu a wasu kananan hukumomin jihar Kano da suka hada da Kiru da Bebeji da Warawa da Dawakin Kudu da Tarauni da kwaryar birni da kuma Dala.
Sauran sun hada da Dambatta da Bichi da Nasarawa, da nufin tabbatar da an yi amfani da kudin da aka ware domin ayyukan mazabu ta hanyar da ta dace.










































