Hukumar DSS ta tsare wani dan takarar gwamnan Kano da wasu mutane 2 domin amsa tambayoyi kan laifin dabar siyasa 

DSS sabo
DSS sabo

 

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a yammacin ranar Talata a Kano, ta kama wani dan takarar gwamna AbdulSalam Abdulkarim Zaura wanda aka fi sani da AA, Zaura, Manajan Daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA), Baffa Baba Dan’agundi da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa, bisa zargin gudanar da ayyukan daba.

Wata majiya mai tushe daga jami’an tsaro ta bayyana cewa, kama shugabannin siyasa a Kano baya rasa nasaba da rikicin da aka yi a wurin taron siyasa a jihar da rikicin da ya barke a Rano a karshen mako da Bichi a ranar Talata.

Majiyar ta ce jami’an hukumar sun yi wa wadanda aka kama tambayoyi na tsawon sa’o’i kafin a sako su a daren ranar Talata.

An ce hukumar ta DSS ta gano makamai a cikin motar wasu ‘yan siyasar da aka kama a lokacin da aka kama su.

Solacebase ta ruwaito cewa Kano ta sha fama da ‘yan bangar siyasa da ke barazana ga zaman lafiya a tsakanin mazauna yankin a ‘yan kwanakin nan inda ‘yan siyasa da dama a jihar ke kokarin fada da juna ta hanyar amfani da ‘yan daba a lokutan tarukan siyasa.

Fadan da aka yi a ranar Asabar ya yi sanadin mutuwar mutane hudu a filin wasa na Rano a wani rikici da ya barke tsakanin magoya bayan wasu ‘yan siyasa a lokacin kaddamar da shugabannin jam’iyyar APC da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi da kuma rikicin da ya barke a Bichi a ranar Talata.

Ko da yake hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutum guda a rikicin siyasa da ya barke a Rano a karshen mako.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here