Hukumar DSS ta gayyaci shugabannin kananan 2 a Kano domin amsa tambayoyi, inda ake neman guda daya ruwa a jallo

DSS
DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama shugaban karamar hukumar Gwarzo da karamar hukumar Birni, Bashir Abdullahi Kutama da Faizu Alfindiki bisa zargin yin amfani da ‘yan bangar siyasa a jihar.

An tattaro cewa a baya-bayan nan ne aka kashe kimanin Mutane uku a yayin gudanar da taron siyasar Gwamna Abdullahi Ganduje a wasu kananan hukumomin jihar, lamarin da ke barazana ga zaman lafiya a jihar.

Wani babban jami’in DSS da ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce sun kama Faizu Alfindiki Shugaban Karamar Hukumar birnin Kano da Bashir Abdullahi Kutama Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, bisa zargin daukar nauyin ‘yan bangar siyasa a Jihar, wanda ya kai ga hare-hare tare da tayar da tarzoma a jihar

Hukumar ta DSS ta kuma bayyana cewa Khalid Ishaq Diso shugaban karamar hukumar Gwale ta Kano shima ana zarginsa da wannan laifi, yayin da wani Dokta Sabiu SSA ga Gwamnan shi ma jami’an tsaro sun kama shi kan wannan zargi.

Solacebase ta tuna cewa rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan wasu ‘yan siyasa a ranar Asabar a filin wasa na garin Rano da ke karamar hukumar Rano a jihar yayin bikin rantsar da shugabannin jam’iyyar APC ya yi sanadin mutuwar mutane 4 tare da jikkata wasu hudu. Ko da yake hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutum daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here