Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben shekara mai zuwa ta 2023, ya ce jerin sunayen da ake yadawa a shafukan sada zumunta da wallafa wasu a kafafen yada labarai na Internet cewa mabobin kwamitin ne ba da sanin su bane.
Daraktan Yada Labaran kwamitin Mista Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja, inda yace an wallafa wandannan sunayen ne ba da izinin kwamitin ba.
Don haka ya bukaci jama’a da su yi watsi da shi, inda ya kara da cewa shugabancin jam’iyyar da dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu za su kaddamar da kwamitin yakin neman zaben nan gaba a hukumance.
Onanuga ya ce jam’iyyar ta fahimci muradin jama’a a jam’iyyar APC da dan takararta na shugaban kasa.
Sai dai ya bukaci kafafen yada labarai da su yi taka tsantsan wajen yada labaran da ba su dace ba.
A lokacin da yake zantawa da sakataren kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Mista James Faleke, Onanuga ya ce ana ci gaba da samar daraktoci daban-daban na tsarin yakin neman zaben.
Ya ce ana yin hakan ne tare da tuntubar gwamnonin jam’iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki.













































