Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu a ranar Laraba ya nemi afuwa kan kalaman da aka danganta masa dangane da maganar katin zabe na dindindin.
Solacebase ta tuna cewa Tinubu a yayin da yake karbar bakuncin tawagar mata daga sassan kasar nan da suka halarci taron matan jam’iyyar APC a ranar Talata, ya bukace su da su duba halin da katin zabe ke ciki tare da sanya magoya bayansu su kara yin katin zaben domin samun damar kada kuri’a a zabe mai zuwa.
Ko da yake Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta mayar da martani kan wannan sanarwa, inda ta ce katin zabe na dindindin bai kare ba.
Hukumar ta ce wadanda suka yi rajistar zabe ba sa bukatar sake yin hakan saboda katunan nasu na aiki ne a zabe mai zuwa.
A wata sanarwa da mai ba Tinubu shawara kan harkokin yada labarai, Mista Tunde Rahman, ya fitar ta ce: “Nan da nan da aka samu labarin haka, Asiwaju ya nemi afuwa kan furucin da ba daidai ba, kuma ya ji tausayin duk wani rudani da ya haifar.
Sanarwar ta ce ya yi amfani da kalmar ‘expire’ maimakon ya ce mai yiwuwa ne a sabunta katunan.
“Tinubu ya kuma jaddada yabon sag a INEC kan aikin da take yi wajen ganin cewa an gudanar da zabe mai inganci a Najeriya.













































