Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Kwami/Funakaye da Gombe, Yaya Tongo, ya rasu a Abuja.
Tongo, wanda ya lashe zaben Dan Majalisar Tarayya a karkashin tutar jam’iyyar PDP a 2023, kafin daga bisani ya sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC a watan Maris din 2026.
Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Pantami ne ya sanar da rasuwar ta sa a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X da aka tabbatar, @ProfIsaPantami.
Pantami ya rubuta, “Mun rasa wakil mu na Gombe, Kwami, da Funakaye, Hon Yaya Bauchi Tongo, wanda ya rasu yau, Juma’a, 12 ga Yunin 2026.”
Tsohon ministan ya ce ya ziyarci dan majalisar a ranar Juma’a da sassafe a Asibitin Nizamiye da ke Abuja, inda yake jinya.
“A yau, tare da Alhaji Bappa Ahmad Abdullahi da wasu abokan aikinmu, mun ziyarci Asibitin Nizamiye da ke Abuja davkarfe 3:30 na yamma inda na yi masa addu’a.
“Kuma na hadu da abokinsa, ‘ya’yansa biyu da sauran ‘yan uwa a asibitin. Sun tarbe ni, suka raka ni har dakin sa.
“‘Yan sa’o’i kadan bayan haka, na samu labarin rasuwar sa a Asibitin yau Juma’a.
Pantami ya kuma kawo maganar Annabi Muhammad SAW wajen tabbatar da maganar sa.
“Annabi Muhammad SAW ya ce ‘babu wanda ya rasu a ranar Juma’a, ko dare ta, sai Allah ya kare shi daga jarabawar kabari,’” in ji shi.
Ya kuma yi addu’a ga marigayin, yana rokon Allah ya yi masa rahama ya sa Aljannatul Firdausi, “Tare da iyayen mu da ‘yan uwa da suka riga mu gidan gaskiya, kuma ya ba iyalin sa da ‘yan uwan sa hakuri.”













































