Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da mutuwar Manjo Janar Rabe Abubakar (Mai ritaya), wanda ya rasu yana hannun ‘yan bindiga bayan watanni na kokarin tabbatar da sakinsa.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron da Al’amuran Cikin Gida, Dr Nasiru Mu’azu, ya fitar a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce tsohon sojan ya mutu sakamakon matsalolin cutar ciwon suga da hauhawar jini yayin da yake tsare.
“Cikin bakin-ciki da jimami muke tabbatar da mutuwar Janar a hannun ‘yan bindiga, duk da kokarin da Gwamnatin Jiha da hukumomin tsaro daban-daban suka yi ba dare ba rana domin tabbatar da sakinsa lafiya, lamarin ya kare da wannan bakin cikin,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta ce sace marigayin da mutuwarsa daga baya asara ce mai girma ga iyalansa, Jihar Katsina da kasar baki daya.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya mika ta’aziyyarsa ga iyali da ke cikin bakin ciki da ‘yan Najeriya, inda ya bayyana lamarin a matsayin “lokaci bakin ciki” kuma tunatarwa kan bukatar hadin kai wajen magance rashin tsaro.
Gwamnatin jiha ta ce za ta ci gaba da aiki tare da Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an gurfanar da masu hannu a wannan laifi gaban shari’a.
Ta kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa kudurin ta na magance matsalar ‘yan bindiga da kare rayuka da dukiyoyi a fadin jihar ba zai ragu ba.
Mutuwar babban jami’in sojan da ya yi ritaya ta sake nuna kalubalen tsaron da ke ci gaba da addabar wasu sassan Arewacin Najeriya, duk da kokarin da hukumomi ke yi na shawo kan ‘yan bindiga da kuma tabbatar da sakin wadanda aka sace.












































