Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi rashin mai ba shi shawara na musamman kan hulda da jama’a, Alhaji Abdussalam Abiola Abdullateef.
Majiya daga ‘yan uwa sa ta shaida wa SolaceBase cewa Abdussalam ya rasu ne a ranar Asabar bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya kuma an binne shi da yammacin ranar a makabartar Hajji Camp.
Karin karatu: Shugaban hukumar REMASAB Danzago ya rasu
SolaceBase ta ruwaito cewa mashawarcin na musamman dan asalin jihar Osun, ya kammala karatunsa ne a fannin lissafi a Jami’ar Bayero Kano, kuma kwanan nan ya yi ritaya daga aiki a Asibitin kashi na Orthopedic da ke Dala a Kano.