Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Gombe, Jamil I. Gwamna, ya yi alkawarin samar da jagoranci mai adalci da zai hada kowa, na amana idan aka zabe shi a babban zaben 2027.
Dr. Gwamna ya fadi hakan ne a cikin jawabin karbar takara a ranar Juma’a bayan nasarar zama dan takarar gwamna na jam’iyyar APC gabanin zaben 2027.
“Na ji dadin amana da girman alhakin da aka ba ni ta hanyar zaben da aka yi min a matsayin dan takar gwamna na APC gabanin babban zaɓen 2027,” in ji shi.
Ya bayyana fitowarsa a matsayin babban nauyi kuma ya yi alkawarin tabbatar da amana da mambobin jam’iyya da magoya baya suka ba shi.
Dan takarar na APC ya kuma yaba wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa jagoranci mai ma’ana da himma ga ci gaban jihar da ya nuna.
A cewarsa, gwamnatin Yahaya ta samu nasarori a fannin ababen more rayuwa, lafiya, ilimi, aikin gona, tsaro, da ci gaban dan adam, wadanda suka kara karfafa amincewar jama’a ga jam’iyyar mai mulki.
Dr. Gwamna ya gode wa shugabannin APC, masu ruwa da tsaki, ‘yan takara, da magoya baya a fadin jihar bisa sadaukarwa da gudummawar da suka bayar a dukkanin tsarin zaben fidda gwani.
“Nasarar gudanar da wadannan zabukan fidda gwanin, taa sake nuna cewa APC a Jihar Gombe jam’iyya ce da aka gina kan tattaunawa, tafiya da kowa, gaskiya, da mutunta shiga cikin harkokin dimokuradiyya,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga sauran ‘yan takara da magoya bayan jam’iyya da su watsar da sabanin da ya
Dr. Gwamna ya tabbatar wa mazauna jihar cewa zai kasance mai saukin samu kuma ya himmatu wajen yi wa kowa hidima yadda ya kamata, ba tare da la’akari da jam’iyya, kabila, ko matsayi ba.
Ya kara bayyana kwarin gwiwar cewa APC za ta yi nasara a zaben 2027 kuma za ta ci gaba da gina kan ginshikin da gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya ta kafa.












































