Dubban mambobin jam’iyyar APC a Jihar Yobe sun bayyana goyon bayansu ga Baba Malam Wali bayan kammala zaben fidda gwanin gwamna na jam’iyyar gabanin babban zaben 2027.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Abdulmumin Kolo Gulani ya fitar a ranar Juma’a a madadin Kungiyar Yada Labarai ta Yakin Neman Zabe na Baba Malam Wali bayan kammala zaben fidda gwani a fadin jihar.
A cewar sanarwar, an samu fitowar al-umma da dama a yayin zaben fidda gwanin jam’iyyar a dukkan yankuna uku na jihar.
Sanarwar ta nuna cewa sakamakon da aka samu daga mazabu 178 ya nuna yawan goyon baya ga Baba Malam Wali a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2027.
An ce magoya bayan jam’iyya da mambobin APC sun bayyana kwarin gwiwa kan halayen jagoranci na dan takarar, kwarewarsa ta siyasa, da iya ci gaba da shirye-shiryen ci gaban da gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ta samu.
Masu ruwa da tsaki sun yaba kan yadda aka gudanar da zaben cikin lumana da girmama juna da mambobin jam’iyyar suka nuna, sun bayyana APC ta Yobe a matsayin daya daga cikin rassa masu hadin kai da tsari na jam’iyyar mai mulki a kasar.
Da yake mayar da martani kan sakamakon, Baba Malam Wali ya gode wa mambobin APC a fadin jihar bisa amana da goyon bayansu.
“Zaɓen yau ya nuna a fili cewa mambobin APC a fadin Jihar Yobe sun hada kai kuma sun himmatu wajen ci gaban jam’iyyarmu, yawan goyon bayansu da karfafawa abin da zai kara mana karfin gwiwa baki daya,” in ji shi.
Dan takarar na APC ya kuma yi kira ga sauran ‘yan takarar da su hada hannu da shi da jam’iyyar domin inganta rayuwar jama’ar jihar.












































