Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta hana Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) amincewa ko shiga kowane taro a jihohi da kwamitocin da shugabancin riko na jam’iyyar ADC ya nada suka shirya.
Da yake yanke hukunci a ranar Laraba, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta bayyana cewa alhakin gudanar da tarukan jihohi yana hannun kwamitocin zartarwa na jihohi na jam’iyyar, ba shugabancin kasa ba.
Kotun ta kara da cewa wa’adin shekaru hudu na kwamitocin aiki na Jihohi da kwamitocin zartarwa na jihohi na ADC yana nan daram, har sai an gudanar da taruka da aka kafa yadda ya kamata da kuma kiran babban taron kasa.
Mai Shari’a Abdulmalik ta kuma bayyana cewa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da na jam’iyyar bai baiwa kwamitin rikon kwarya, karkashin jagorancin David Mark, ikon nada kwamitoci don gudanar da tarukan jihohi.
Hukuncin na karar mai lamba FHC/ABJ/CS/581/2026 da Don Norman Obinna, Johnny Tovie Derek, Obah C. Ehigiator, Hon. Olona Yinka, Dr. Charles Idowu Omideji, Samuel Pam Gyang, da Obianyo Patrick suka shigar a matsayin masu kara, suna kara wa kansu da kuma a madadin duk Shugabannin Jihohi da kwamitocin zartarwa na jihohi na am’iyyar ta ADC.
Cikin wadanda ake karar akwai Jam’iyyar ADC, Sanata David Mark, Sanata Patricia Akwashiki, Mallam Bolaji Abdullahi, Ogbeni Rauf Aregbesola, Farfesa Oserheimen Osunbor (a madadin kwamitin rikon kwarya) da INEC.
Masu karar sun koka, a tsakanin sauran abubuwa, cewa shugabancin ADC karkashin Mark ya kafa kwamitin taro don gudanar da tarukan jihohi.
Inda suka kalubalanci sahihancin duk wani nadi da kwamitin rino na Mark ya yi kuma sun bayar da hujjar cewa shirin gudanar da tarukan jihohi a watan Afrilu 2026, idan aka gudanar da shi karkashin kulawar wannan kwamitin rikon, zai zama babban laifi a kundin tsarin mulkin jam’iyyar.











































