Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, ta umarci Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) a ranar Talata da ta mika Ifeanyi Onyewuenyi, jami’in ta da ake zargi da sace wata matashiya Walida Abdulhadi ya kuma yi amfani da karfi ya yi mata ciki ga ‘yan sanda don gudanar da bincike.
A baya dai, an zargi Onyewuneyi ya sace Walida ‘yar shekara 16 daga karamar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa, ya yi mata fyade kuma ya tilasta mata shiga addinin Kirista watanni da suka wuce.
Daga baya Walida ta haifi jaririya mace, amma bayan Allah wadai da matsin lambar jama’a, hukumar ta DSS ta mika matashiyar ga gwamnatin jihar Jigawa.
Sai dai, yayin da yake yanke hukunci a ranar Talata, Mai Shari’a Hassan Dikko ya ba da umarnin a saki matashiyar ba tare da wani sharadi ba kuma ya umarci DSS da ta mika Onyewuenyi ga ‘yan sanda don cikakken bincike.
Hukuncin ya kuma yi watsi da duk wani bincike na cikin gida da DSS ta ce ta gudanar a baya, inda bayyana ayyukan hukumar a matsayin kokarin kare jami’inta daga fuskantar shari’a.
Mai shari’a Dikko ya bayyana zargin da ake yi a matsayin “abin Allah wadai,” yana mai jaddada tsananin zarge-zargen.
Lauyan dangin matashiyar, Kabiru Adamu, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ba ga wadanda yake karewa ba kawai, har ma ga bin doka da oda.
Ya ce, “Wannan hukunci yana kara karfafa kwarin gwiwar jama’a ga bangaren shari’a a matsayin sa rai na karshe ga talaka.”
Ya bukaci ‘yan sanda da su tabbatar da gaskiya da gaggauta bincike da zarar an mika musu wanda ake zargin.
Tun da fari dai, wata Kotun Majistare a Hadejia ta ba da umarnin a saki matashiyar kuma a mika wanda ake zargin ga ‘yan sanda, umarnin da DSS ta kalubalanta a babbar kotun tarayya.











































