Da ɗumi-ɗumi: Mataimakin gwamnan Kano Aminu Gwarzo ya yi murabus

Aminu Gwarzo 750x430

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Gwarzo, ya yi murabus daga mukaminsa.

Murabus ɗin na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dokokin jihar ke shirin tsige shi daga mukamin, bayan ta aike masa da takardar zargin da ta bukaci ya kare kansa cikin makonni biyu kan wasu zarge-zargen almundahanar kudi.

A kokarinsa na dakatar da shirin tsigewar, mataimakin gwamnan ya garzaya kotun tarayya inda ya nemi umarnin gaggawa na hana aiwatar da shirin, amma kotun ta ƙi amincewa da bukatar tare da umartar lauyansa ya sanar da sauran bangarorin da ke cikin karar.

Rikicin siyasa a Kano ya fara ne bayan gwamna Abba Kabir Yusuf tare da wasu ‘yan majalisa suka fice daga NNPP zuwa APC.

Sai dai Gwarzo ya ki bin wannan tafiya, inda ya dage kan biyayya ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya da kuma NNPP.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun tafiyar Kwankwasiyya, Dakta Habibu Sale Mohammed ya fitar, ya bayyana cewa wannan mataki an dauke shi ne domin amfanin al’umma da kuma tabbatar da zaman lafiya da daidaiton mulki a jihar Kano.

Sanarwar ta bayyana cewa halin da ake ciki a baya-bayan nan ya takaita yadda mataimakin gwamnan zai iya gudanar da aikinsa yadda ya kamata, don haka ya zama dole a bar mukamin ya ci gaba da aiki yadda ya dace domin amfanin jama’a.

Haka kuma an tabbatar da cewa murabus din ba yana nufin ya amince da zarge-zargen da ake yi masa ba, inda ya nace cewa aikinsa a gwamnati da hidimar jama’a na nuna gaskiyarsa da jajircewarsa.

Sanarwar ta kara da cewa ya dauki wannan mataki ne domin nuna kwarewa a siyasa da kuma kauce wa rikice-rikicen da ka iya kawo cikas ga shugabanci da ci gaban jihar.

Haka zalika, Gwarzo ya kuduri aniyar mayar da hankali kan tafiyar Kwankwasiyya, musamman wajen karfafa tsarinta da shirye-shiryen siyasa gabanin zabukan shekarar 2027.

An kuma bukaci magoya bayan tafiyar da al’ummar Kano da su kasance masu bin doka da oda tare da ci gaba da goyon bayan nagartaccen shugabanci da dimokuradiyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here