Wasu ƙarin ‘yan Najeriya 125 sun dawo daga Sudan.
Mutanen waɗanda jirgin Tarco B737-300 ya ɗauko daga Port Sudan sun sauka a filin jirgin saman Abuja da tsakar ranar Asabar.
A yanzu adadin ‘yan Najeriya da aka kwaso daga Sudan ya kai 2,371.
Jami’an shige da fice da na hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA, da jami’an hukumar kula da ‘yan gudun hijira ne suka tarbe su a filin jirgin.
A ranar uku ga watan Mayu ne jirgin farko ɗauke da ‘yan Najeriya Sudan ya sauka a filin jirgin Abuja.
Tun daga ranar ne kuma ake ta jigilar ƙwasar ɗaliban waɗanda suka maƙale a ƙasar sakamakon faɗan da ya ɓarke tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF masu sanye da kayan sarki.













































