Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, murnar cika shekara 63 a duniya.
A cikin sakon taya murna da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta da aka tantance, jagoran tafiyar Kwankwasiyya ya yi addu’ar Allah Ya ƙara masa hikima, lafiya da kuma tsayuwar manufa a sabuwar shekarar rayuwarsa.
Kwankwaso ya waiwayi doguwar tafiyar siyasar da suka yi tare da gwamnan Kano tsawon shekaru da dama, inda ya bayyana irin rawar da Abba Kabir Yusuf ya taka a matakai daban-daban na mulkinsa.
Ya bayyana cewa Abba Kabir Yusuf ya fara aiki a matsayin mataimakinsa na musamman a wa’adinsa na farko da kuma lokacin da yake minista, sannan ya zama babban mataimaki na musamman, daga bisani kwamishina a wa’adinsa na biyu, kafin daga ƙarshe ya zama gwamnan Jihar Kano.
A cewarsa, duk waɗannan muƙaman sun ba Abba Kabir Yusuf damar ba da gagarumar gudunmawa wajen aiwatar da hangen nesa da shirye-shiryen da suka shimfiɗa domin ci gaban Jihar Kano.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Abba Kabir Yusuf, wanda shi kaɗai ne gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, ana danganta shi da yunƙurin ficewa daga jam’iyyar zuwa APC, lamarin da wasu kalaman Rabiu Musa Kwankwaso na baya-bayan nan ke nuna cewa akwai saɓani a kai.













































