Rundunar ’yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da sace wani gogaggen ɗan jarida mai ɗaukar hoto, Malam Umar Usman a cikin jihar Kaduna, abin da ya jefa al’umma da ’yan uwa cikin damuwa.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN game da sace ɗan jaridar a ranar Talata a Kaduna.
Ya bayyana cewa rundunar ta riga ta ƙaddamar da bincike domin gano inda aka kai Malam Umar Usman cikin koshin lafiya ba tare da wani lahani ba.
Ya bayyana cewa an sace ɗan jaridar da misalin ƙarfe tara na dare a ranar Litinin, a unguwar Danhonu II da ke Millennium City, a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, daga gidansa, wanda tsohon ma’aikaci ne a gidan talabijin na AIT reshen Kaduna, sannan kuma ya taɓa aiki a Hukumar Talabijin ta Ƙasa NTA reshen Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar ya bayyana cewa kwamishinan ’yan sanda na jihar Kaduna, Malam Rabiu Muhammad, ya gaggauta tura tawagar jami’ai domin bin sawun masu garkuwa da mutane tare da tabbatar da an ceto Malam Umar Usman cikin koshin lafiya.
Rundunar ’yan sandan ta kuma yi kira ga al’ummar yankin da su bayar da duk wani sahihin bayani da zai taimaka wajen gano inda aka kai ɗan jaridar da kuma ceto shi cikin gaggawa.
NAN













































