Rundunar ’yan sandan Nijeriya da ke sashen filin jirgin sama, ta cafke wani matashi mai shekaru 20 da ake zargi da aikata damfarar mutane da dama a ƙasar Amurka sama da Naira Biliyan ɗaya.
Mai magana da yawun rundunar a sashen filin jirgin sama, ASP Mohammed Adeola, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a jihar Lagos.
Ya bayyana cewa an cafke wanda ake zargin ne a ranar Litinin bayan da jami’an sashen yaƙi da zamba na rundunar ’yan sanda a filin jirgin sama suka kama shi yayin da yake shirin hawa jirgi ya bar jihar Lagos.
Ya ce cafke wanda ake zargin ya biyo bayan watanni na tattara bayanan sirri da sa ido bisa sahihan bayanai da suka danganta shi da wasu manyan laifukan zamba a ƙasashen ƙetare.
Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin, wanda a baya yake zaune a Calabar, ya koma jihar Lagos a ranar 23 ga Fabrairu, 2024, inda daga nan yake tsarawa tare da aiwatar da wasu ayyukan zamba da dama da suka shafi mutanen da ke Amurka.
Karanta: ’Yan sanda sun tabbatar da sace ɗan jarida a jihar Kaduna
A wani babban lamari a shekarar 2024, binciken ya nuna cewa wanda ake zargin ya yaudari wata mata ’yar shekaru 47 a Amurka, inda ta tura masa Dala Miliyan ɗaya da nufin sayen gida a jihar Florida domin gina gidan marayu.
Sai dai an samu kuɗaɗen ne ta hanyar wata dabara ta kuɗin intanet da ake kira BullRun 2.0, wadda a baya ake kira 4 Way Mirror Money.
Har ila yau, bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya sake damfarar wata mata ’yar shekaru 70 a Amurka, inda ya karɓi Dala 18,000 da darajarsu ta kai kusan naira Miliyan 26.
Wanda ake zargin ya aiwatar da zambar ne ta hanyar sayen katunan kyauta, wayoyin zamani masu tsada da kayan kwamfuta, waɗanda aka turo zuwa Nijeriya bisa umarnin wanda ake zargin.
Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da kwamfutar MacBook Pro mai inci 14, iPhone 17 Pro Max, wayoyin Google Pixel 10 Pro XL guda biyu da kuma Google Pixel 10 Pro guda ɗaya, waɗanda jimillar darajarsu ta kai Naira 8,141,367.
Bincike ya kuma gano cewa wanda ake zargin yana kwaikwayon kansa a matsayin likitan ƙashi mai shekaru 60 da ke aiki tare da Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya.
Adeola ya bayyana cewa kwamishinan ’yan sanda na sashen, Olufunke Ogunbode, ta jaddada ƙudirin rundunar na hana masu laifi amfani da filayen jirgin sama a matsayin hanyar tserewa ta hanyar amfani da bayanan sirri.
Ya ƙara da cewa rundunar za ta ci gaba da amfani da dabarun bayanan sirri domin ganowa, tarwatsawa da rusa hanyoyin aikata laifi a cikin da wajen harkar sufurin jiragen sama a Nijeriya.
A cewarsa, an mika wanda ake zargin tare da kundin shari’arsa zuwa sashen yaƙi da manyan laifukan zamba na rundunar ’yan sandan Nijeriya domin ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu daga bisani.
NAN













































