Dakarun rundunar Sojin Nijeriya na Operation Fansan Yamma, sun dakile wani yunƙurin fashin hanya a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, lamarin da ya hana aukuwar lahani ga matafiya.
Wata majiya daga rundunar ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Talata, bayan sojojin sun samu kiran gaggawa daga yankin Nasarawan Doka.
Majiyar ta bayyana cewa sojojin sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka tunkari masu aikata laifin tare da dakile barazanar da suka haifar.
An kama wani daga cikin waɗanda ake zargi, mai suna Kabiru Zayyanu, wanda ya samu raunin harbin bindiga a ƙafa, sannan aka kai shi babban asibitin Doka domin samun agajin farko.
Sauran ’yan kungiyar sun tsere daga wajen da lamarin ya faru, yayin da sojojin suka ci gaba da binsu cikin gaggawa ba tare da sake haɗuwa da su ba.
Majiyar ta tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ko sace mutane ba a yayin wannan aiki, kuma za a mika wanda aka kama ga hukumomin da suka dace bayan kammala bincike.
Ta ƙara da cewa yanayin tsaro a yankin ya kasance cikin kwanciyar hankali, inda sojoji ke ci gaba da kasancewa a wurin tare da mamaye yankin.
NAN










































