JOHESU ta soki matakin garambawul na shekarun ritaya da gwamnatin tarayya ta yi a ɓangaren lafiya

JOHESU

Gamayyar ƙungiyoyin ma’aikatan lafiya ta ƙasa JUHESU ta soki sabuwartakardar umarni da gwamnatin tarayya ta fitar game da gyaran shekarun ritayar ma’aikatan lafiya a Nijeriya, inda ta yi gargaɗin cewa tsarin yana fifita rukuni guda ne kawai a cikin ma’aikatan lafiyar ƙasar.

Kungiyar ta bayyana cewa wannan mataki na barazana ga adalci, haɗin kai da kuma ingancin aikin ba da kulawar lafiya, domin tsarin kiwon lafiya ba ya tafiya ne bisa rukuni ɗaya kawai ba.

A wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta aikewa ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati na tarayya, ƙungiyar ta nuna damuwa mai tsanani kan yadda aka aiwatar da tsarin, tana mai cewa an karkatar da manufar da aka tsara tun farko domin amfanar da dukkan ma’aikatan lafiya.

Kungiyar ta tuna cewa tsawon fiye da shekaru goma sha biyar ita ce ke jagorantar fafutukar neman ƙara shekarun ritayar ma’aikatan lafiya, kasancewar wannan buƙata ta kasance muhimmin ɓangare na yarjejeniyoyin fahimtar juna guda takwas da aka kulla da gwamnatin tarayya daga shekarar 2014 zuwa 2024.

Ta bayyana cewa batun ya sake fitowa fili a tattaunawar da ta biyo bayan yajin aikin watan Yuni na shekarar 2023, inda ta bayyana cewa a jami’o’i da cibiyoyin da ke da alaƙa da su, ana barin ma’aikata su yi ritaya a shekara 65, yayin da malamai masu mukamin farfesa ke yin ritaya a shekara 70.

Kungiyar ta ce duk da ƙin amincewa da shawararta a lokuta da dama, har zuwa watan Disamba na shekarar 2025, shiga tsakani da ta yi ne ya kai ga samun amincewar shugaban ƙasa, amma daga bisani ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta kwace tsarin, inda aka kafa wani kwamiti da ya karkata tsarin tsawaita shekarun ritaya domin amfanar likitoci kaɗai.

Kungiyar ta yi gargaɗin cewa wannan tsari na wariya zai lalata kwarin gwiwar ma’aikata, ya hanzarta ficewar gogaggun ma’aikata daga tsarin kiwon lafiya, tare da karya tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 da aka yi wa gyara.

A saboda haka ta bukaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya umarci fitar da sabon takardar umarni mai adalci da ya shafi dukkan ma’aikatan lafiya ba tare da nuna bambanci ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here