Wata babbar kotu a Kano ta soke matakin rushe kwamitocin shugabanni na jiha, ƙananan hukumomi da unguwanni na jam’iyyar NNPP a Kano, tare da rusa hukuncin da kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar ya yanke.
Kotun ta bayar da wannan umarni ne ta hanyar hukuncin gaggawa da Mai shari’a Nasiru Saminu ya yanke, inda ya hana kwamitin gudanarwa na ƙasa na NNPP ɗaukar duk wani mataki dangane da tsarin shugabancin jam’iyyar a Kano har sai an saurari kuma an yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an shigar da ƙarar mai lamba K/06/2026 ne daga Abdullahi Zubairu Imam da wasu mutane biyar, a madadin kwamitin shugabannin NNPP na ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, inda suka kalubalanci rushewar shugabancin da jam’iyyar ta yi.
A cikin umarnin wucin gadi, kotun ta kuma umarci dukkan ɓangarorin da abin ya shafa su ci gaba da bin tsarin da ake kai a ranar 30 ga Disamba, 2025, kafin fitar da umarnin rushewar shugabannin daga kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar.
Kotun ta kara hana jam’iyyar, wakilanta ko duk wani kwamiti da ke aiki a madadinta, nada kwamitocin rikon ƙwarya a matakin jiha, ƙananan hukumomi da unguwanni a Kano, tare da umarnin a kai takardun ƙarar zuwa sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja.
Idan za a iya tunawa cewa kwamitin gudanarwa na ƙasa na NNPP ya sanar da rushe shugabannin jam’iyyar a dukkan matakai a Kano ne bayan dakatar da Hashim Dungurawa daga matsayin shugaban jam’iyyar na jiha, inda aka maye gurbinsa da Abdullahi Abiya a matsayin shugaban riko.













































