Rundunar ‘yan sandan jihar Niger ta gano wani abin fashewa da ake zargin na soja ne wanda bai tashi ba a yankin Zugurma da ke ƙaramar hukumar Mashegu ta jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Minna.
Ya bayyana cewa gano abin fashewar ya biyo bayan wani rahoto da rundunar ta samu daga jami’in kula da ofishin ‘yan sanda na shiyyar Ibbi da ke Mashegu, bayan wasu mazauna yankin sun hangi wani abu da ake zargin makami mai linzami ne a cikin daji a yankin.
Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda daga shiyyar sun isa wajen cikin gaggawa tare da killace yankin domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Karanta: ’Yan sanda sun tabbatar da sace ɗan jarida a jihar Kaduna
Kakakin rundunar ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adamu Elleman, ya bayar da umarnin tura jami’ai zuwa wurin, inda sashen kwararru na rundunar ‘yan sanda kan kawar da bama-bamai da abubuwan fashewa, da sinadarai, halittu, hasken nukiliya da makaman nukiliya, EOD-CBRN, karkashin jagorancin CSP Mohammed Mamun, suka isa wurin.
Ya kara da cewa jami’an shiyyar tare da hadin gwiwar al’ummar yankin sun jagoranci tawagar zuwa ainihin inda aka samu abin, inda aka tabbatar da cewa abin fashewar makami ne na soja da bai tashi ba, aka kwance shi lafiya tare da kai shi hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar da ke Minna, yayin da bincike ke ci gaba kan asalin abin.
NAN













































