Najeriya ta Doke kasar Egypt da ci 2-4 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
An dai fafata wasan a filin wasa na Casablanca’s Stade Mohammed V a ranar Asabar 17/01/2026
Nasarar da Najeriya din ta samu ya sanya ta kare a matsayin ta 3 a gasar cin kofin Africa wato (AFCON) da ake fafatawa a kasar Morocco.
An kwashe muntuna 120 ana fafata wasan babu kasar da ta samu nasarar zura kwallo a ragar abokiyar karawarta hakan ne yasa aka tafi bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Yan wasan na Super Eagles na Najeriya dai sun buga kwallo mai kyau a wasan kamar yadda suka buga a fafatawar da sukai da kasar Morocco wanda suka yi rashin nasara a bugun na daga kai sai mai tsaron raga hakan ne ya hana su zuwa wasan karshe a gasar.
A gobe Lahadi 18/01/2026 ne dai za a fafata wasan karshe na gasar tsakanin kasar Morocco da take karbar bakuncin gasar da kuma kasar Senegal a filin wasa na Rabat da ke kasar.












































