Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya NiMET ta yi hasashen samuwar hazo tare da hasken rana daga ranar Laraba zuwa Juma’a a dukkan sassan ƙasar.
Hasashen yanayin da hukumar ta fitar a ranar Talata ya nuna cewa za a samu yanayi mai ɗauke da hasken rana da hazo a tsawon kwanakin da aka ambata a Arewacin Kasar nan.
A cewar hukumar, yankunan arewacin ƙasar za su kasance cikin yanayin hasken rana tare da hazo a duk tsawon lokacin hasashen.
Hukumar ta yi hasashen cewa yankunan kudancin ƙasar za su samu sararin sama mai hasken rana tare da ɗan taruwar gajimare, kuma akwai yiwuwar samun tsawa a wurare kaɗan tare da ruwan sama mara yawa a wasu sassan jihohin Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom da Cross River daga bisani a cikin rana.
Rahoton ya nuna cewa wannan yanayi zai ci gaba ba tare da wani babban sauyi ba a yankin arewa.
Hukumar ta bayyana cewa irin wannan yanayi na faruwa ne sakamakon sauyin yanayi da ke shafar iskar da ke yawo a sararin samaniya.
Ta ƙara da cewa jama’a su kasance masu lura da yanayin da ke gudana tare da ɗaukar matakan kariya da suka dace yayin wannan lokaci.













































