Kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bayar da beli ga tsohon Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya Abubakar Malami SAN, tare da ɗansa Abubakar Abdulaziz da matarsa Hajia Bashir Asabe, inda kotun ta sanya musu beli na Naira Miliyan 500 kowannensu tare da masu jingina biyu-biyu a daidai wannan adadi.
Alkalin kotun Emeka Nwite ya yanke wannan hukunci a ranar Laraba, yana mai cewa hujjojin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Tarayya ta gabatar domin hana belin ba su da ƙarfi da za su hana kotu amincewa da bukatar.
Alkalin ya bayyana cewa dalilan da hukumar ta gabatar sun karkata ne zuwa zato kawai, ba tare da gamsasshen tushe na doka ba.
Saboda haka, kotun ta amince da belin tare da sharadin cewa masu jinginar su kasance masu mallakar kadarori a yankunan Asokoro, Maitama ko Gwarimpa a cikin Babban Birnin Tarayya.
Alkalin ya umarci cewa dole ne mataimakin magatakardar shari’a na sashen ƙara na kotun ya tantance takardun mallakar kadarorin da aka gabatar.
Kotun ta kuma umarci Malami, matarsa da ɗansa da su miƙa dukkan fasfofin tafiyarsu na ƙasashen waje ga mataimakin magatakardar shari’a na sashen ƙara, tare da hana su fita daga ƙasar ba tare da izinin kotu ba.
Karanta: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan bukatar beli da Abubakar Malami ya gabatar
Haka kuma, an umarce su tare da masu jinginar su da su ajiye hotunan fasfo biyu-biyu a hannun magatakardar kotu, sannan a tabbatar da ingancin wuraren zamansu ta hannun magatakardar kotu.
Alkalin Emeka Nwite ya kuma umarci waɗanda ake tuhuma da su ci gaba da kasancewa a gidajen gyaran hali na Kuje da Suleja har sai sun cika dukkan sharuddan belin da aka gindaya.
Daga nan ne kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 17 ga Janairu domin fara sauraron shari’a.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa EFCC ta shigar da tuhume-tuhume a kan Malami, matarsa Hajia Bashir Asabe, ɗansa Abubakar Abdulaziz, da kuma wani ma’aikacin wani kamfani da ake dangantawa da tsohon ministan, Rahamaniyya Properties Limited, inda aka sanya su a matsayin waɗanda ake tuhuma na farko, na biyu da na uku.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa a cikin tuhume-tuhume guda 16, ta zargi waɗanda ake tuhuma da aikata mu’amaloli masu cike da shakku da kuma ƙoƙarin ɓoye asalin Biliyoyin Naira ta hanyar asusun banki da sayen kadarori a Abuja, Kano da Kebbi tsakanin shekarun 2015 zuwa 2025, wanda ya haɗa da shekaru takwas da Malami ya yi yana aiki a matsayin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a zamanin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Hukumar ta ce sun haɗa kai wajen ɓoye asalin kuɗaɗe, sayen kadarori ta bayan fage da kuma riƙe kuɗaɗen da suka san sun fito ne daga haramtattun hanyoyi, abin da ya saɓa wa dokokin hana safarar kuɗaɗe na shekarar 2011 da aka yi wa gyara da kuma na 2022.
A cikin ƙidayar tuhume-tuhumen, EFCC ta zargi Malami da ɗansa da ɓoye sama da Naira Biliyan ɗaya a asusun bankin Sterling tsakanin Yuli 2022 da Yuni 2025, da kuma ɓoye fiye da Naira Miliyan 600 tsakanin Satumba 2020 da Fabrairu 2021 ta wani kamfani.
Haka kuma, an zarge su da amfani da Naira Miliyan 600 a matsayin jinginar kuɗi don rancen Naira Miliyan 500, da kuma sayen gidaje masu tsada a Maitama, Asokoro, Garki, Jabi da Gwarimpa a Abuja, tare da wasu kadarori a Kano da Kebbi, inda ake zargin kuɗaɗen da aka yi amfani da su sun fito ne daga haramtattun hanyoyi.
Hukumar EFCC ta ce ta shirya kiran shaidu da dama ciki har da jami’anta, wakilan bankuna, ‘yan canjin kuɗi da ƙwararrun harkokin kuɗi domin tabbatar da tuhume-tuhumen.
Daga cikin manyan shaidun akwai Folarin Dare, Chinedu Eneanya, Sani Lukeman, Abdulrahman Musa Basheer, Jamilu Mohammed, da wakilan bankunan Zenith da Sterling, inda ake sa ran za su bayyana yadda hukumar ta samu bayanan sirri da ƙorafe-ƙorafen da suka shafi zargin babbar almundahana a kan tsohon ministan, tare da rawar da kamfanin Rahamaniyya Properties Limited ya taka wajen sayen kadarori da ake dangantawa da Malami.













































