Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran Laifuka masu alaka ta (ICPC) ta bayyana cewa za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban kotun tarayya da ke Kaduna ranar Talata, 24 ga Maris, 2026, bisa zargin aikata laifukan da suka shafi rashawa.
A cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar, John Odey, ya fitar, ya bayyana cewa za a gurfanar da El-Rufai tare da wani Joel Adoga a cikin shari’ar da ke dauke da lamba FHC/KD/73/2026 a gaban kotun tarayya da ke sashen shari’a na Kaduna.
Hukumar ta ce tuhume-tuhumen sun haɗa da karkatar da dukiyar jama’a da mallakar kadarorin gwamnati ba bisa ka’ida ba, da kuma wankiyar kuɗi.
Haka kuma, hukumar ta bayyana cewa akwai wata shari’a ta daban mai lamba KDH/KAD/ICPC/01/26 da aka shigar a gaban babbar kotun jihar Kaduna, wadda ta shafi El-Rufai da wani Amadu Sule (LEDA).
A cewar ICPC, tuhume-tuhumen da ke cikin wannan shari’ar ta jihar sun haɗa da cin zarafin ofis, zamba, yunƙurin aikata zamba da kuma bai wa wasu gata ba bisa ka’ida ba, inda aka shigar da dukkanin tuhume-tuhumen a ranar 18 ga Maris, 2026.
Hukumar ta kuma bayyana cewa an riga an mika takardun sammaci ga El-Rufai, tare da jaddada cewa za ta bi dukkan matakan doka yadda ya kamata.
Idan za a iya tunawa, an tsare El-Rufai a hannun EFCC a ranar 16 ga Fabrairu, sannan aka ba shi beli a ranar 18 ga Fabrairu, amma nan take ICPC ta sake cafke shi, kuma tun daga lokacin yake tsare a hannunta yayin da ake ci gaba da kira da a gurfanar da shi a kotu.













































