ICAN ta fara bincike kan bidiyon bogi da ya nuna ana rubuta jarrabawar bogi

ICAN 750x430 (1)

Ƙumgiyar ƙwararrun Akantoci ta Najeriya (ICAN) ta fara bincike kan wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, da ake zargin ya nuna bogi a cikin ɗaya daga cikin jarrabawarta.

Bidiyon ya nuna wani ɗalibi da aka kama yana rubuta jarrabawar ICAN a madadin wani kwamishinan kuɗi daga yankin arewa maso gabas.

A cikin faifan bidiyon, masu kula da jarrabawa sun tambayi wacce ake zargi, wadda ta bayyana kanta da sunan Leavitt Felix.

Da yake mayar da martani, Babban Sakataren gudanarwa na ICAN, Lanre Olasunkanmi, ya bayyana cewa hukumar na da tsayayyen tsari na rashin yarda da duk wani nau’in saɓon jarrabawa, ciki har da bogi.

Ya ce tsarin jarrabawar ICAN yana kan ka’idojin amana da gaskiya da aka amince da su a duniya, kuma duk wani yunƙurin karya wannan tsari ana ɗaukar shi da matuƙar muhimmanci.

Olasunkanmi ya ƙara da cewa an riga an fara bincike sosai a kan lamarin, kuma za a ɗauki matakan ladabtarwa bisa ga ƙa’idojin da aka shimfiɗa, tare da sanar da sakamakon ga al’umma da masu ruwa da tsaki.

Hukumar ta kuma roƙi jama’a da su guji yin zato ko yanke hukunci bisa bayanan da ba su da tabbas, tana mai tabbatar da cewa ICAN za ta ci gaba da kare sahihancin jarrabawarta da mutuncin aikin lissafi a Najeriya da wajen ƙasar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here