Masu bore sun sace kundin tsarin mulki

IMG 20230109 WA0003
IMG 20230109 WA0003

Kotun kolin kasar Brazil ta tsige gwamnan jihar Brasilia daga mukaminsa na tsawon kwanaki 90, sakamakon kura-kuran da aka samu kan tsaro a babban birnin kasar, bayan da dubban magoya bayan tsohon shugaba Jair Bolsonaro mai ra’ayin rikau suka kai wa gine-ginen gwamnati hari.

Alkalin kotun kolin Alexandre de Moraes ya kuma umarci dandalin sada zumunta na Facebook da TikTok da su dakile duk wani yunkuri na yada farfagandar juyin mulki.

Tuni dai mahukuntan kasar Brazil suka fara gudanar da bincike kan harin mafi muni da aka kai kan cibiyoyin gwamnatin kasar, tun bayan da aka maido da dimokradiyya shekaru arba’in da suka gabata, inda shugaba Luiz Inacio Lula da Silva ya sha alwashin gurfanar da wadanda suka haddasa tarzomar to gaban kuliya.

Dubun dubatar masu zanga-zangar adawa da sabuwar gwamnati ne a ranar Lahadin da ta gabata suka mamaye gine-ginen kotun koli, Majalisar dokoki da kuma sassan fadar shugaban kasa tare da farfasa tagogi, da hautina kayan daki, tare da sace kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1988.

Rahotanni sun kuma ce masu boren sun kwace bindigogi daga ofishin tsaron fadar shugaban kasa.

Shugaba Lula mai ra’ayin gurguzu, wanda ya hau kan karagar mulki a ranar 1 ga watan Janairu, ya ce rundunar ‘yan sandan garin Brasilia da ta kai rahoton ga gwamnan Brasilia Ibaneis Rocha, wanda tsohon abokin Bolsonaro ne, bai yi wani abin da ya hana masu zanga-zangar ci gaba da tayar da hankali ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here