Gwamnan Kano ya bayar da umarnin farautar wanda ya kashe uwa da ’ya’yanta 6

Abba Kabir Yusuf Kano Kano 715x430

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna matuƙar alhini kan kisan gilla da aka yi wa wata mata da ’ya’yanta a unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin ƙyama, marar tausayi kuma babban tauye martabar ɗan Adam.

Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, inda gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, al’ummar Dorayi Chiranchi da kuma daukacin jama’ar jihar Kano, tare da yin addu’ar Allah Ya gafarta wa mamatan Ya kuma ba iyalansu juriyar jure wannan babban rashi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa kisan uwa da ’ya’yanta marasa laifi abu ne da ba za a taɓa amincewa da shi ba, tare da cewa gwamnatinsa ba za ta bari irin wannan mummunan laifi ya wuce ba tare da hukunci ba.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa gwamnan ya bayar da umarnin gaggawa ga rundunar ’yan sandan jihar Kano da su bazama farautar masu aikata laifin tare da tabbatar da cafke su da gurfanar da su gaban shari’a, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da hannu a ciki zai fuskanci hukuncin doka ba tare da sassauci ba.

Karin bayani: Kano: An yiwa wata Mata da yara shida mummunan kisan gilla

Haka kuma, gwamnan ya umarci hukumar tsaron ta Neighbourhood Corps da su ƙara yawan sintiri da sa ido a unguwanni masu rauni, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa tsaro a matakin al’umma da kuma hana sake faruwar irin wannan ibtila’i.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu, su ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai, tare da gaggauta kai rahoton duk wani abu da ake zargi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati ta kuduri aniyar kare rayuka da dukiyoyin jama’a a kowane lokaci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here