Kano: An yiwa wata Mata da yara shida mummunan kisan gilla

WhatsApp Image 2026 01 17 at 17.26.42 540x430

Mazauna unguwar Dorayi Chiranchi da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano sun shiga firgici a yammacin ranar Asabar bayan wasu da ba a san ko su wanene ba suka shiga wani gida suka kashe wata maya da ’ya’yanta shida ta hanyar amfani da makamai masu haɗari.

Lamarin ya faru ne a gidan Haruna Bashir, inda aka kai harin kan Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin alhini da tashin hankali.

Bayan gano gawarwakin waɗanda aka kashe, makwabta sun yi kuwwa abin da ya janyo ruɗani da jimami a fadin unguwar Dorayi Chiranchi.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa daga bisani an kwashe gawarwakin daga wajen da abin ya faru tare da kai su Asibitin Ƙwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.

Bayan aukuwar lamarin, rundunar ’yan sandan jihar Kano ta karɓi kiran gaggawa tare da tura jami’ai zuwa yankin domin gudanar da bincike, inda aka ɗauki matakan tsaro na gaggawa a yankin.

Rundunar ’yan sandan ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan mummunan ta’asa tare da cafke su, kana ta jajanta wa iyalan mamatan, mazauna Dorayi Chiranchi da al’ummar jihar Kano baki ɗaya, tare da tabbatar da cewa za a hukunta masu laifin bisa doka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here